
Kofin Nahiyar Afrika
Kasashen Afrika 28 ne za su kece raini a tsakaninsu a zagaye na 2 na gasar neman cancantar shiga gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika da za a yi badi a kasar Afrika ta kudu daga karshen makonnan.
Daga cikin kasashen akwai Najeriya wadda za ta je birnin Freetown domin karawa da 'yan wasan Leone Stars na Laberiya ranar Assabar, kafin daga bisani 'yan wasan kasar ta Laberiya su zo babban birnin Najeriyar Abuja domin buga bangare na biyu na gasar ranar 12 ga Satumba.
Ranar laraba Shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya kai wata ziyarar ba-zata a wurinda 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Super Eagles ke karbar horo gabanin wasar da zasu buga da kasar ta Laberiya.
''ku cigaba da nuna dagewa da kuma azama, mu kuma zamu cigaba da yin iya kokarinmu a gwamnati domin baku kwarin gwiwa, kuma na tabbata kuma na gamsu cewar za samu nasara a wasar da zaku buga da Laberiya''.injiShugaban wanda ya ziyarci babban filin wasa na kasa da ke Abuja tare da rakkiyar mataimakinsa Muhammed Namadi Sambo.













