
Bukin bude gasar Paralympics ya kayatar
Wani dan Najeriya ya lashe lambar zinare ta farko da wani dan Afrika ya ci a gasar Olympics ta guragu da ake yi London.
Yakubu Adesokan ya lashe lambar zinaren ne a wasan daukar karfe mai nauyin Kilogiram 48 na maza, inda kuma ya karya tarihinda wasu suka kafa a baya a duniya wajen daukar karfen cikin sauri.
Taha Abdulmajid dan kasar Masar ya lashe lambar tagulla a wannan wasan.
Najeriya dai ba ta samu lambar yabo ko daya ba a gasar Olympics da aka kammala a farkon watan nan.













