
Bolaji Abdullahi minista wasannin Najeriya
Kungiyar kwallon kafa ta mata 'yan kasa ga shekaru 20 ta wuce mataki mai bima na karshe na gasar cin kofin duniya ta mata dake akeyi a birnin Tokyona kasar Japan.
Da kyar dai Kungiyar ta Falconet dai ta doke takwararta ta kasar Mexico da ci 1-0 a wasan da suka buga ranar Alhamis, inda har sai da ta kai aka yi karin lokaci.
'yan wasan na Najeriya wadanda suka kai matakin karshe na gasar a kasar Jamus shekaru biyu da suka gabata, sun yi kane-kane a sa'a ta farko ta wasan amma ba su samu damar ci ba har sai a minti na 109.
Desire Oparanozie ce dai ta jefa kwallo a ragar Mexicon.












