
Wayne Rooney
Dan wasan gaba na kulob din Manchester United, Wayne Rooney, na fuskantar zaman benci har tsawon makonni hudu bayan da ya samu rauni a cinyarsa ta dama lokacin wasan da kulob din ya yi da Fulham ranar Asabar.
Rooney ya samu raunin ne a lokacin da dan wasan Fulham Hugo Rodallega ya dira a cinyarsa yayin da ya yi kokarin tare bugun tazara.
An dauki Rooney a kan gadon dauke 'yan wasan da suka yi rauni, kuma ba zai samu damar buga wasanni biyu na neman shiga gasar cin kofin duniya da Ingila za ta yi ba.
Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya ce: "Nan take aka dauke Wayne Rooney zuwa asibiti kuma da alama raunin da ya samu mummuna ne. Ina ganin ba zai buga wasanni ba har tsawon makonni hudu''.













