
Mai horar da 'yan wasan Real Madrid, Jose Mourinho
Mai horar da 'yan wasa na kulob din Real Madrid, Jose Mourinho ya ce sabanin da ya samu da mai horar da 'yan wasa na kulob din Barcelona, Tito Vilanova ba zai yi tasiri a wasan da za su buga a yau ba.
Mourinho ya zunguri kan tsohon mataimakin shugaban Barcelona, yayin da Vilanova shi kuma ya mare shi, hakan ya faru ne a kasar wasannin da ta gabata.
Game da wasan da kulob din biyu za su buga a yau a gasar Super Cup ta Spaniya, Mourinho ya ce " Taka ledar bai shafi Pep ko Tito ba, mun san dai za mu yi wasa ne da barcelona."
Wasan na El-Clasico a farkon gasar Super Cup za a yi kara ne a filin wasa na Nou Camp, yayin da a ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 2012 kuma, filin wasa na Bernabeu zai dau bakuncin wani El-Clasico.
Mourinho ya kara da cewa yana ganin wasan ba zai yi wani tasiri ga kakar wasanni na bana ba, kuma idan yana da zabi da ya fi son Real ta fadi a gasar Super Cup, amma mu yi nasara a gasar La liga, kamar yadda ya faru a bara.


















