
Oussama Assaidi
Dan wasan Kungiyar Heerenveen ta Holland Oussama Assidi dan kasar Morocco zai koma Liverpool kamar yadda kulob din sa ya sanar.
Dan wasan mai shekara 24 wanda zai je Liverpool ta duba lafiyarsa idan yi nasarar binciken zai zama sabon dan wasa na uku da kocin Liverpool Brendan Rodgers ya saya a bana.
Assaidi ya ciwa kungiyarsa kwallaye 20 a wasanni 68 da ya buga mata.
Ya bugawa kasarsa Morocco wasa sau 22 tun lokacin da ya fara yi mata wasa a watan Fabrairu na 2011.
Rodgers ya ce yana saran sayen wasu karin sababbin 'yan wasan daya ko biyu kafin fara wasansu na Premier na bana ranar Asabar da gidan West Brom.
Ana ganin Liverpool za ta sayi dan wasan Barcelona Cristian tello mai shekaru 21 da kuma dan wasan Real madrid Nuri sahin dan shekara 23.













