
Jack Rodwell
Manchester City ta sayi Jack Rodwell daga Everton sai dai ba a bayyana yawan kudin cinikin ba.
Dan wasan mai shekaru 21 wanda Everton ta yi masa kudi fam miliyan 15 kocin Ingila ya zabe shi a cikin wadanda zasu bugawa kasar wasa a karawar da zata yi da Italiya ranar Laraba.
Ana ganin Rodwell zai karawa City karfi a tsakiya saboda rashin Gareth Barry wanda ya yi rauni a kugunsa da kuma rashin tabbas a game da Nigel de Jong a kungiyar saboda yana cikin shekarar karshe ta kwantiraginsa kuma kulob din Bayern Munich ya nuna sha'awarsa ta sayen dan wasan mai shekaru 27.
Rodwell ya fara wasa ne daga reshen matasa na kungiyar Everton tun yana shekara 7, kuma ya bugawa kungiyoyin matasa na kasar Ingila a matakai daban-daban har hudu kafin daga bisani ya fara bugawa babbar kungiyar 'yan wasan Ingilan a karawarta ta sada zumunta da Spain a watan Nuwamba na 2011.












