
Victor Moses
Chelsea ta kusa kammala cinikin da take yi na sayen dan wasan gaban Wigan Athletic, Victor Moses, bayan kungiyoyin sun gama tattaunawa game da sa hannu a kan kwantiraginsa.
Manajan Wigan, Dave Whelan, ya gana da babban jami'in Chelsea, Ron Gourlay, ranar Talata don tattaunawa a kan yarjejeniyar sayen dan wasan mai shekaru 21.
Wigan ta bukaci Chelsea da ta sayi Moses a kan fan miliyan takwas da rabi kamar yadda ta sanya masa farashi tun da farko.
Har yanzu dai Chelsea na san ran cewa Moses zai buga mata wasa a gasar wasan shekara-shekara na kulob-kulob din kasashen da suka lashe gasar zakarun Turai ranar Lahadi, inda za su kara da kulob din Manchester City.
Whelan ya ce duk da yake ba ya so Moses ya bar kulob din, amma kulob din ba zai hana shi komawa babban kulob ba idan yana son yin hakan.












