bbc.co.uk navigation

West Ham ta hakura da neman Andy Carroll

An sabunta: 6 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 22:24 GMT
andy carroll

Andy Carroll

Duk da cewa Liverpool da West Ham sun amince Andy Carroll zai koma West Ham a matsayin aro akan fam miliyan 2, dan wasan mai shekaru 23 ya shedawa West Ham da ta sami cigaba zuwa rukunin Premier cewa ba shi da niyyar komawa kungiyar.

Tsohuwar kungiyarsa ta Newcastle har yanzu ta na son shi, sai dai ba za ta biya kudin da West Ham take bukata a kan dan wasan da ita ta saida wa Liverpool fam miliyan 35 a 2011 ba.

Yayin da ya rage kasa da mako biyu a fara kakar wasanni ta bana ba a san makomar dan wasan ba kawo yanzu.

Dan wasan dai yana cigaba da yin atisaye a Liverpool da fatan raunin da ya ji a matsematsinsa zai warke.

Ba a sani ba dai ko zai buga wasan da liverpool zata yi da kungiyar Gomel a Anfield na neman shiga gasar cin Kofin Europa ranar Alhamis wanda daman Liverpool ta na da kwallo daya a ragar Gomel din a karawar da suka yi mako biyu da suka wuce.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2013 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.