BBC navigation

Messi ya kafa tarihin zura kwallo

An sabunta: 21 ga Maris, 2012 - An wallafa a 12:58 GMTLionel Messi ya kafa tarihi na zura kwallaye da ba'a samu irinsa ba a shekaru sittin da suka gabata a klub din Barcelona.

Messi ya kafa tarihin ne bayan zura kwallaye uku a wasan da Barcelona ta doke Granada a Nou Camp da aka tashi ci biyar da uku a gasar La Liga ranar Talata.

Kwallon da Messi ya zura a mintuna 17 da fara wasan ne yasa ya yi daidai da tarihin da aka kafa a shekaru sittin da suka wuce, sannan ya kara zura wata a mintuna 68 abinda ya kaishi kafa sabon tarihi.

An dai rage darajar tarihin da ya kafa zuwa 232 daga 235 bayan wani nazari da wata jarida ta yi.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.