bbc.co.uk navigation

Pearce ya nuna kwadayin jagorantar Ingila a Euro 2012

An sabunta: 23 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 17:23 GMT

Kocin Ingila na wucin gadi, Stuart Pearce

Kocin Ingila na wucin gadi Stuart Pearce ya ce zai iya jagorantar kasar zuwa gasar cin kofin Turai da za'a shirya a kasar Poland da Ukraine.

Kocin wanda har wa yau shi ke jagorancin tawagar 'yan kasa da shekaru 21 ya gayyato Fraizer Campbell da kuma Tom Cleverley cikin 'yan wasan kasar da za su buga wasan sada zumunci da Holland a filin Wembley a ranar Laraba mai zuwa.

"Ina da gogewa a manyan gasa irin wannan, kuma idan suna bukatata, zan karbi aikin." In ji Pearce.

A baya dai kocin ya nisanta kansa da karbar aiki a matsayin na dindindin bayan da aka Sallami Fabio Capello a watan da ya gabata.

"Wannan aikin na bukatar wanda ya kware, kuma ina da gogewar da zan iya daukar aikin a yanzu haka." In ji Pearce.

Kocin Tottenham, Harry Redknapp dai na daya cikin wadanda ake hasashen za su jagoranci tawagar ta Ingila, amma Pearce ya ki ya ce uffan game da maganar.

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.