
Kocin Tottenham, Harry Redknapp
Kocin Tottenham, Harry Redknapp ya ce baya tunanin maye gurbin Fabio Capello, kuma ya nace cewa zai maida hankali ne a kungiyar Tottenham.
Kocin Tottenham din wanda ya bayyana hakan ga manema Labarai ya ce; "Ina fatan duk matakin da hukumar FA ta dauka na nada sabon kocin zai yi dai-dai.
"Ina jin dadin aiki da Tottenham, kuma bai kamata inyi tunanin wani abu a yanzu haka ba sai Tottenham."
Hukumar FA dai ta bada tabbacin cewa ba tuntubi Harry Redknapp ba, game da wasan maye gurbin Capello.









