
Jose Mourinho, kocin Real Madrid
Jose Mourinho ya ce wasu daga cikin 'yan wasansa a Real Madrid sun yi imanin cewa babu yadda za su yi nasara a filin Barcelona na Nou Camp.
Barcelona dai ta fidda Real Madrid ne a gasar Copa del Rey bayan da kungiyoyin biyu su ka tashi biyu da biyu a Nou Camp.
A bugun farko da kungiyoyin biyu su ka yi Barcelona ce ta yi nasara a filin Real Madrid wato Barneabue da biyu da daya.
An dai nunawa 'yan wasan Real Madrid katin gargadi takwas a wasan, kuma an nunawa Sergio Ramos biyu abun da kuma ya sa aka sallame shi.
Mourinho ya ce: "Na ji yadda wasu 'yan wasanna ke cewa babu yadda za su yi nasara a Nou Camp saboda alkalan wasa basa musu aldalci.".
"Akwai kuma kurakurai da dama da alkalin wasa ya tafka abun da kuma ya shafi makomarsu.
"Zan jinjinawa Barcelona ne kawai saboda nasarar da su ka yi a gidanmu, amma ba dan tsallakewa zuwa zagaye na gaba ba."
"Na sha wasa a filin na Nou Camp, tun ina Chelsea da Inter Milan duk lamarin daya ne.
Real Madrid dai ta yi nasara sau daya a kan Barcelona a kara goma sha hudu da kungiyoyin biyu su ka yi.







