An sabunta: 11 ga Satumba, 2011 - An wallafa a 12:58 GMT

US Open: Nadal ya fidda Murray a wasan kusa da na karshe

Rafeal Nadal bayan ya yi nasara akan Andy Murray

Rafeal Nadal ya lallasa Andy Murray a gasar Tennis ta US Open inda yi nasara a wasanni hudu a wasan kusa dana karshe a gasar.

A yanzu haka dai Rafeal Nadal zai kara ne da Novak Djokovic a wasan karshen a ranar Litinin.

Novak Djokovic dai ya doke Roger Federer ne shima a wasan kusa dana karshe.

Nadal ya doke Murray ne da maki 6-4 6-2 3-6 6-3 a wasan da suka buga na tsawon sa'a uku da minti 24.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.