BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 05 Mayu, 2010 - An wallafa a 14:38 GMT
 
Aika ýmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Tsarin dimokradiyyar Burtaniya
 

 
 
Shugaban jam'iyyar Conservative David Cameron
Shugaban jam'iyyar Conservative David Cameron
Sabanin kasashen irinsu Amurka da Najeriya da sauran kasashe dake bin tsari irin na shugaba mai cikakken iko, Burtaniya tana bin tsari ne irin na majalisa.

Tsari ne da ke da wasu ginshikai da suka hadar da shugaban kasa amma na jeka na yi ka, sai shugaban gwamnati wanda aka fi sani da Pira minista.

Wanda a lokuta da dama kan kasance jagoran jam'iyyar da ta fi rinjaye a majalisa, da kuma majalisar zartarwa, wadanda mambobinta kan kasance manyan 'yan majalisar dokoki.

A daya bangaren kuma, wani babban ginshiki na wannan tsarin shi ne 'yan majalisar dokoki na bangaren adawa.

Majalisun dokoki

Tsarin gwamnatin burtaniya dai ya hadar da majalisun dokoki guda biyu, wadanda ake kira House of Comons wato majalisar dokoki inda Pira minista da 'yan majalisar zartarwarsa ke zama da sauran 'yan majalisu da suka hadar da 'yan adawa.

Da kuma House of Lords wato majalisar dattijai, wadanda yawancin mambobinta nada su ake yi ko kuma su yi gadon kujerarsu.

A tsarin majalisa irin na Burtaniya a kowanne lokaci za a iya rusa gwamnati a kuma kira wani zaben idan an gamu da wani cikas.

Irin tafarkin da Burtaniya ke gudanar da al'amuran demokaradiyyarta dai na da sarkakiya ainun, domin shugabar kasar watau sarauniyar Ingila tana da matsayi ne tamkar na jeka na yi ka, duk da cewa ko me za a yi da sunan gwamnatinta ake yi.

Yadda ake gudanar da al'amura

Pira Minista dai shi ke gudanar da al'amuran yau da kullum na gwamnati tare da hadin gwuiwar 'yan majalisa.

Wani abu da yake masu sharhi ke cewa ya banbanta tsarin mulki irin na majalisa da kuma na shugaba mai cikakken iko shi ne irin yadda a lokuta da dama 'yan majalisa musamman na bangaren adawa kan titsiye Pira minista da tambayoyi musamman a kan manufofin da suke ganin sun saba da na jam'iyyarsu.

Duk jam'iyyar da ta samu rinjaye a zaben 'yan majalisar dokoki dai ita ke kafa gwamnati. Kuma a kashegarin ranar zabe, sarauniyar Ingila ta kan gayyaci jagoran jam'iyyar domin ya zama pira minista ya kuma kafa gwamnati.

Sai dai idan jagoran jam'iyyar ya rasa kujerarsa ta dan majalisa a zaben da aka gudanar, to jam'iyyarsa za ta nada wanda zai rike jagoranci na wucin gadi wanda shi ne sarauniya za ta gayyata don kafa gwamnati kafin jam'iyyar ta zabi wani sabon jagora.

 
 
David Cameron na jam'iyyar Conservative Nazari kan shirin zaben Burtaniya
Zaben Burtaniya 2010
 
 
Gordon Broww Jam'iyyun Burtaniya da akidun su
Akawi yiwuwar ayi kan-kan-kan
 
 
David Cameron na Conservative Nazari kan muhawarar karshe ta zaben Burtaniya
Ranar zabe kawai ake jira
 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ýmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri