BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 04 Mayu, 2010 - An wallafa a 09:49 GMT
 
Aika ýmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Jam'iyyun Burtaniya da akidun su
 

 
 
 yanzu jam'iyyar Conservative ce a gaba
A yanzu jam'iyyar Conservative ce a gaba
Yayin da ya rage saura kwanaki kadan al'ummar Birtaniya su kada kuri'unsu, manyan jam'iyyun siyasar kasar na ci gaba da kara azama wajen yakin neman zabe. Ko yaya dai sakamakon zaben ya kaya a wannan karon, za'a kafa tarihi.

Jam'iyyu da dama ne dai ke fafatawa a zaben, sai dai an fi mayar da hankali ne a kan manyan jam'iyyun kasar guda uku, wato Labour mai mulki, da kuma babbar jam'iyyar adawa ta conservative, da kuma Libral Democrat wanda ta samu gagarumin tagomashi a yakin neman zaben na bana.

Kowacce jam'iyya dai na kokarin janyo hankalin masu zabe domin su kada mata kuri'a bisa la'akari da akidu da manufofin da ta kafu a kansu. To ko wadanne akidu jam'iyyun suke kokarin karewa?

Jam'iyyu kimanin arba'in ne dai ke takarar kujeru daban daban a zaben gama gari da ake shirin gudanarwa a nan Burtaniya ran Alhamis shida ga wannan watan.

Sai dai jam'iyyu uku ne ke kan gaba a jerin wadanda ake ganin za su iya kafa gwamnati a zauren Majalisar Westminister dake Birnin London inda akan gudanar da muhawarori masu zafi tsakanin Pira Minista Gordon Brown na jam'iyyar Labour da kuma David Cameroon na Conservative, jam'iyyu biyun dai su ne suka fi yawan kujerun a majalisar da ta gabata.

Jam'iyya ta uku a yawan kujeru ita ce Libral Democrat, kuma jam'iyyun uku su ke gaba gaba a fafatawar kafa gwamnati a wannan zaben.

Manufofi

Jam'iyyun uku dai na da manufofi da suka sha banban da juna, kuma an kafa su ne a kan akidu maban banta.

An kafa jam'iyyar Labour wadda Pira Minista Gordon Brown ke jagoranta ne sakamakon gwagwarmayar kungiyoyin kwadago fiye da shekaru dari da suka gabata. Jam'iyyar ta kuma samu mukamin minista na farko ne bayan yakin duniya na daya, kuma jam'iyyar ta samu wata nasarar bazata da ta baiwa su kansu 'ya'yanta a shekarar 1945.

Gordon Brown na tsaka mai wuya

Jam'iyyar Labour kamar yadda sunanta ke nuna wa, ta kafu ne a kan akidar kare manufofin ma'aikata, sai dai kwanci tashi, ta yi ta sauya manufofinta inda a shekarun 1990 ta yi bankwana da ra'ayin gurguzu ta kuma rungumi matsakaicin ra'ayin sauyi, inda ake wa jam'iyyar take da New Labour wato sabuwar jam'iyyar Labour.

Karkashin wannan tsarin Pira Minista na lokacin Tony Blair, ya ce jam'iyyar za ta mayar da Burtaniya kasa ta zamani, mai samar da daidaito a tsakanin al'umma, kuma babu wata alfarma da za a yi wa ma'aikata da suka kafa ta, yayinda jam'iyyar za ta rungumi 'yan kasuwa don kawo ci gaba a kasar.

Jam'iyyar Labour wadda ta shafe shekaru goma sha tara tana mulki, a yanzu tana kokarin kare kujerun da take da su masu rinjaye ne a majalisa, sai dai matsin tattalin arziki da kuma sauyi da wasu 'yan kasar ke kokarin samu na barazanar hana mata mayar da wannan rinjayen, abin da ya sa ake ta hasashen samun ratayayyar majalisa, wato Hung Parliament.

Jam'iyyar Tory ko conservative kamar yadda ta fi shahara a yanzu, za ta iya bugar kirji ta ce ita ce jam'iyya mafi dadewa a turai.

A karni na goma sha bakwai, Tory kamar yadda ake kiranta a wancan lokacin ta goyi bayan gidan sarautar burtaniya ta zama mai sanya ido a kan ayyukan majalisa.

A gargajiyance dai jam'iyya ce da ake danganta wa da wadanda suka mallaki filaye ko gonaki da kuma masu hannu da shuni, sai dai a baya bayan nan ta dage tana neman goyon bayan mutane daga kowanne sashe na al'umma.

Ana yiwa jam'iyyar kallon mai sassauci daga akidunta na jari hujja a yanzu, kuma kuma bayan ta shafe shekaru goma sha tana adawa, binciken jin ra'ayoyin jama'a daban daban sun nuna cewa jam'iyyar na iya samun nasara a zabe mai zuwa, ko kuma alal akalla, ta yi kan kan kan da jam'iyyar Labour mai mulki.

Bazata

Kwatsam sai ga Liberal Democrat ta kunno kai.

A cewar shugaban jam'iyyar Liberal Democrat Nick Klegg, makwanni kalilan da suka gabata, jama'a sun dauka zaben na bana zai kasance ne tsakanin manyan jam'iyyu biyu da aka saba, sai dai an samu sauyi, inda a yanzu aka samu jam'iyya ta uku.

An dai kafa jam'iyyar wadda a da aka fi sani da Libral party ne a shekarar 1886 wato fiye da shekaru dari da ashirin da suka gabata.

Jam'iyyar liberal Democrats dai ta sha ganin samu ta ga rashi a siyasar Burtaniya. kuma kamar yadda sunan jam'iyyar ya nuna, an gina ta ne a kan sassaucin ra'ayi, da kuma baiwa kowa 'yancin ya zabi abin da yake so.

Tauraruwar jam'iyyar ta kara haskakawa ne a zaben bana, bayan rawar ganin da shugabvanta Nick Klegg ya taka a muhawarorin da aka gudanar tsakanin jagororin jam'iyyu uku na kasar.

A yanzu da ake ta maganar yiwuwar samun ratayayyar majalisa, inda babu jam'iyyar dake da rinjaye, hankali ya karkata ga jam'iyyar ta Liberal Democrat, don sanin wadanda za ta mara wa baya tsakanin Labour ko Conservative domin kafa gwamnati idan har ba a samu jam'iyya daya da ta yi rinjaye a zaben ba.

 
 
Gordon Brown Shirin Zaben Birtaniya
Birtaniya za ta fara gudanarda zabe a ranar shida ga watan Mayu
 
 
Gordon Brown da abokinsa Obama Jam'iyyar labour ta kaddamar da yakin neman zabe
tattalin arziki ne a gaba
 
 
Shugaban jam'iyyar Conservative David Cameron Jam'iyyar Conservative ta kaddamar da yakin neman zabe
kawo sauyi ne a gaba
 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ýmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri