 |
|
| Obama da Thein Sein |
Shugaban Amurka Barrack Obama yayi kira ga Firimiyan kasar Burma Janar Thein Sein da a saki mai faftukar dimukuradiyya ta
kasar, Aung San Suu Kyi.
Shugaban na Amurka ya mika wannan sako ne a wata ganawa da yayi tare da shugabani goma na yankin Asiya Pacific, a kasar Singapore.
Wata sanarwa da aka fitar bayan taron ta nemi a yi adalci a zaben da aka shirya gudanarwa a kasar ta Burma a cikin shekara
mai zuwa.
Wakiliyar BBC tace amincewar da shugaba Obama yayi ya shiga tattaunawar da ta kunshi jami'an soji na kasar Burma, wata babbar
alama ce ta sauyin manufofin Amurka.
|