BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 15 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 20:26 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Switzerland ta Lashe Gasar 'Yan Kasa da Shekaru 17
 
Kwalloin Kafa
Kwalloin Kafa
Kasar Switzerland ta lashe kofin kwallon kafa na duniya a gasar wasan kwallon kafa ta yan kasa da 17. Switzerland ta fitar da Nigeria ne da ci daya da nema.

Yayin da Nigeria ta zo ta biyu a wannan gasa da kasar ta dauki bakuncin shiryawa, kasar Spain ta zo ta ukku bayan da ta fitar da Columbia da ci daya da nema.

An dai kammalla gasar ta cin kofin kwallon kafa na duniya ta 'yan kasa da shekaru 17 lami lafiya.

An gudanar da gasar ce a filayen wasanni na Abuja, Lagos, Ijebu-Ode, Enugu, Calabar, Bauchi, Kano da Kaduna.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri