BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 14 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 20:12 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Gwamnatin Zambia ta Koka Kan Bincike
 
Rupiah Banda, Shugaban kasar Zambia
Rupiah Banda, Shugaban kasar Zambia
Shugaba Rupia Banda na Zambia yace gwamnatin kasar ta kashe kimanin dala miliyan goma sha ukku wajen binciken tsohon shugaban kasar Frederick Chiluba, saboda zargin barnatar da rabin dala miliyan guda.

Wata kotu a kasar dai ta wanke Mr Chiluba da zargi a watan Agusta.

Shugaba Banda ya bayyanawa wani gangami cewa za a iya amfani da wadannan kudade wajen inganta makarantu, da kuma harkokin kiwon lafiya da asibitoci.

A wani batun na daban wata kotu a London ta yanke hukuncin samun Mr Chiluba da laifin zambatar kasar ta Zambia kudaden da yawansu ya kai dala miliyan arba'in ta hanyar amfani da wasu bankuna a London.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri