BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 14 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 14:48 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Sabuwar Majalisa a Niger
 
Malam Tanja Mamadou
Malam Tanja Mamadou
A Jamhuriyar Niger an kaddamar da sabuwar majalissar dokokin kasar karkashin sabuwar Jamhuriyar da Shugaba Malam Tandja Mamadou ya bullo da ita, wadda ta bashi damar zarcewa akan karagar mulki.

Wannan majalissar dokoki ita ce ta farko a karkashin jamhuriya ta 6.

Majalissar ta kunshi yan majalissu 113 da suka hada da mata 11.

Jam'iyyun adawa na Niger sun kauracwa zaben yan majalissar dokokin suna cewar ya sabawa doka.

Kungiyar Ecowas ko Cedao ta dakatar da jamhuriyar Niger daga cikin kungiyar a sakamakon gudanar da zaben yan majalissar dokokin.

An kaddamar da majalissar ce a lokacin da kungiyar Ecowas ke tattaunawa da bangarorin siyasar Niger da nufin warware rikicin siyasar da ake fama da shi.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri