 |
|
| Sojojin Birtttania a Basra |
Ma'aikatar harkokin tsaro ta Birtaniya ta ce tana gudanar da bincike akan wani sabon zargi da ake yiwa sojojin kasar cewar
sun ci zarafin wasu mutane a Iraqi, lokacin da yankin Basra ke hannunsu.
Lauyoyin da ke wakilatar mutanen da aka ci zarafi sun bayyanawa jami'an Birtaniya kararraki na cin zarafi har guda talatin
da uku wadanda suka ce sun bayyana tun bayan da dakarun Birtaniya suka janye daga Basra a watan Yuni.
Daya daga cikin zargin ya shafi fyaden wani yaro dan shekaru 16 da wasu sojojin Birttaniya 2 suka yi.
Lauyoyin sun yi kiran a gudanar da cikakken bincike na bainar Jama'a akan wannan zargi.
|