|
Zabe na gari a Najeriya, ina mafita?
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsarin mulkin dimokradiya tsari ne da ya tanadi gudanar da zabe na gari.
To amma wasu na ganin matsalolin da suka dabaibaye tsarin na dimokradiyya a Najeriya su ne kan hana gudanar da zabe na gari. Saboda wannan dalili ne wasu al'ummar kasar ke ganin ya kamata a yi watsi da dukkan abubuwan da kan haifar da nakasu ga dimokuradiyya a kasar domin jama'a su zabi wadanda za su mulke su. Malam El Harun Muhammad, malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, ya bayyanawa wakilin BBC cewa hatta tsarin jam'iyyun kasar bai yi la'akari da bukatun al'umma ba. "Yadda aka tsara jam'iyyun siyasan kansu, da wadanda ke cikin jam'iyyun siyasan a matsayin jami'ai, da abubuwan da jam'iyyun siyasan suka sa a gaba...duk an yi wadannan ne ba tare da la'akari da hakikanin meye matsalar kasar ba", inji shi. Ina mafita? Shi kuwa Barista Muhammad Musa Soba, mai magana da yawun jam'iyyar AC a Jihar Kaduna, cewa laifin rikirkita al'amuran zabe a kasar na dukkan 'yan siyasan kasar ne: "Duk wadanda suka tsinci kansu a mulki...kusan abin da suke yi iri daya ne". Don ganin an gyaro harkar zabe a kasar, Dokta Abubakar Sadik, malami a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya ce wajibi ne "mutane su kare kuri'unsu idan suka kada; su tabbatar abin da suka kada shi ne aka shaidawa jama'a". Amma a cewar Alhaji Ya'u Usman Jama'a, Shugaban Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kaduna, mafita ita ce "kowa ya yarda da Allah, ya yarda cewa mulkin nan daga Allah ya ke. Komai karfinka, komai kudinka, komai yawan jama'arka, in Allah Ya ce ba za ka yi ba, ba ka isa ka yi ba. In ba ka da ko kwabo, Allah Ya ce kai rubutacce ne sai ka yi mulki a lokaci kaza, wallahi sai ka yi". |
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||