BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 11 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 21:18 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
An Tuna da Wadanda Yaki ya Kashe
 
A ranar da kasashe da dama ke bikin tunawa da mutanen da suka mutu a lokutan yaki, Shugaban Amurka, Barak Obama, ya karrama mamatan ne tare da dora wani katon tarde na furanni a kabarin dogon yaro a makabartar kasa ta Arlington.

Shugaba Obama ya yaba ma sojojin Amurka na yanzu da cewa sun kare kasar daga hadurra, sun kuma baiwa Amurkawa damar samun kyakykyawar rayuwa.

Kafin sannan a ranar a birnin Paris, shugabannin kasashen Faransa da Jamus, sun halarci bikin tare a karon farko, a ranar da ake kira ta kwance damara, bayan kawo karshen Yakin Duniya na Daya.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri