|
Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afrika, ECOWAS ko CEDEAO, a yau Abuja, sun bayyana
cewa za su hada kai wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa da kuma ingantaccen tsaro a yankin yammacin Afrika.
Sun kuma nuna damuwa a kan rikicin siyasar da ake fama da shi a Jumhuriyar Niger da Guniea.
Kana sun jadada muhimancin ganin Jumhuriyar Nijar ta koma kan turbar kiyayewa da sahihan dokokin kasar.
Sai dai kuma sun nuna goyon bayansu ga tattaunawar da ake yi a Abuja karkashin jagorancin Janar Abdusalam Abubakar Mai Ritaya
da masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar kasar ta Nijar.
|