|
Yan sanda a arewa-maso-yammacin Pakistan sunce, akalla mutane ashirin da hudu ne suka rasa rayukansu, a wani harin bam da
aka kai a garin Charsadda, dake arewacin Peshawar.
Shugaban yan sandan Charsadda, Riaz Khan ya ce bisa bayanan da su ka samu daga asibiti, kimanin mutane goma sha biyar ne aka
kashe, yayin da ashirin da biyar zuwa talatin suka ji raunuka.
Jami'an sun ce an kai harin bam din ne cikin wata mota a kusa da wata kasuwa mai yawan hada-hadar jama'a.
Wannan shi ne harin bam na uku cikin 'yan kwanaki da aka kai a yankin Peshawar, wajen dake kusa inda dakarun Pakistan ke gumurzu
da 'yan Taliban.
|