BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta:
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Shugaba Obama ya Ziyarci Sansanin Fort Hood
 
Shugaba Obama ya kai ziyara a sansanin sojan Fort Hood da ke Texas, inda a makon jiya wani jami'in soja, Manjo Nidal Hasan, ya bindige mutane sha ukku.

A lokacin addu'o'in tunawa da matattun, shugaba Obama ya ce, wani mummunan abu ne ya faru, saboda an kashe su ne a kasar Amirka, ba wai a fagen daga ba.
Ya kuma sha alwashin gudanar da cikakken bincike akan abinda ya faru.

Masu gudanar da bincike na Amirka na duba yiwuwar ko akwai wata alaka tsakanin sojan da ake zargi da kashe mutanen, da kuma wani malamin Islama mai tsattsauran ra'ayi da ke Yemen.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri