 |
|
| Charles Taylor |
Tsohon shugaban Liberia, Charles Taylor ya ce hukumonin Nijeria ne suka yaudare shi har aka kama shi, aka kuma gurfanar da
shi a gaban shari'a.
Mr Taylor ya bayyana haka ne a bahasin da ya bayar a shari'ar da ake yi masa a a kotun musamman mai hukunta laifuifukan yakin
Saliyo a birnin Hague.
Yana fuskantar shari'a ne bisa zargin rawar ya taka wajen bada goyon baya ga 'yan tawayen Saliyo, wadanda suka tafka ta'asa
a lokacin yakin basasar kasar a shekarun 1990.
Mr Taylor yana gudun hijira ne a Nijeria, lokacin da aka kama shi a shekara ta 2006.
Ya ce shugaban Nijeria na wancan lokaci, Olusegun Obasanjo ya fada ma sa cewa yana iya ficewa daga kasar ba tare da wata matsala
ba, amma kuma sai ya sa aka cafke shi bisa yunkurin arcewa daga kasar.
|