 |
|
| Babban Bankin Nijeria ya kawo sauye-sauye da dama |
Babban bankin Nijeriya wato Central Bank ya gabatar da wani sabon shiri na bunkasa tattalin arzikin kasar.
A karkashin sabon shirin da gwamnan babban bankin Malam Sanusi Lamido Sanusi zai jagoranta, za a samar da wani kamfani wanda
zai lura da bankunan da suke fama da matsalar basussuka.
Hakanan kuma babban bankin tare da ma'aikatar kudi ta Nijeriyar, za su bayar da gudunmawa, wadda zaa hada da alkawarin da
gwamnatin tarayya ta yi na biyan wadanda suke bin gwamnati basussuka domin samar da kudade kusan Naira biliyan dari biyar
domin bunkasa tattalin arzikin na Nijeria.
|