 |
|
| An Fatattaki Mayakan Al-Qaeda daga Afghanistan |
Shugaban rundunar sojan Birtaniya, Sir Jock Stirrup, ya ce a halin yanzu, kungiyar Al-Qaeda ba ta gudanar da aikace aikacenta
a cikin Afghanistan, kuma an tilasta mata ficewa daga kasar zuwa wani dan karamin tsuki a cikin kasar Pakistan.
Sir Jock Stirrup ya kara da cewa, gaskiya ne a cikin yan shekarun da suka wuce, ginshikan kungiyar ta Al-Qaeda sun fuskanci
mummunan cikas. To sai dai ba wai an rabu da Bukar ba ne.
Wata kuri'ar neman ra'ayin jama'a da BBC ta shirya ta nuna cewa, yawan mutanen Birtaniya masu goyon bayan yakin da sojojin
kasar ke yi a Afghanistan ya ragu.
|