|
Ana ci gaba da fuskantar matsaloli wajen shige da ficen kayayyaki tsakanin Nigeria da Niger tun kusan mako guda kenan. Hukumomi
sun ce suna gudanar da bincike.
Wasu 'yan kasuwa, musamman ma direbobi masu dakon kaya, da al'ummomi mazauna yankunan kan iyakokin, wadanda ke raja'a akan
harkar kasuwanci suna ci gaba da kokawa da al'amarin.
Wakilin BBC da ya ziyarci garin Faru na jihar Maradi, a kan iyakar Niger da Nigeria, ya ce ya tarar da motoci na sauke lodi,
'yan kasuwar kuma na ta kuminiya da kayan da suka dauko.
Lamarin ya daure wa jama'a kai, saboda basu san dalilin daukar wannan matakin ba.
|