BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 08 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 16:34 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
China Zata ba Kasashen Afirka Matalauta Bashi
 
China zata ba kasashen Afirkar da suka fi fama da talauci, wasu sabbin basusukan da suka kai dala bilyan goma, a shekaru ukku masu zuwa. Gwamnatin Chinar zata kuma yafe wasu basusukan da take binsu.

Praministan kasar ta Sin ne, Wen Jiabao, yayi sanarwar a taron kolin da Chinar ke yi da kasashen Afirka, a wurin shakatawa na Sharm El Sheikh da ke kasar Masar.

Da ma dai China ta zuba jari na biliyoyin daloli a kasashen Afrikar, amma tana shan suka, kan yadda take yin biris da batutuwan tauye hakkin jama'a, a kokarinta na samun albarkatun da Allah ya horewa nahiyar Afirkar.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri