BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 07 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 07:46 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Taron G20 A Scotland
 
Ministocin kudi na kasashen duniya guda ashirin da suka fi karfin tattalin arziki (G20) na taro a St Andrews, Scotland, don tattaunawa a kan batun farfadowa daga matsalar tattalin arzikin da duniya ta fada ciki da kuma kudin da ake bukata don magance matsalar sauyin yanayi.

Yayin da tattalin arzikin duniya ke kara samun daidaito a 'yan watannin nan, masu zuba jari da dama na kara zuba jari a kasuwannin hada-hadar kudade na kasashe masu tasowa.

Wannan na faruwa ne sakamakon kwarin gwiwa da masu zuba jarin su ke sake samu da kuma rage kudin ruwa da manayan bankuna suka yi a kasashe masu wadata.

Sai dai wannan ya sa wasu kasashe masu tasowa sun fara nuna damuwa. Kwararowar wadannan kudade ya sa darajar kudaden kasashen masu tasowa ta hauhawa, abin da ke sa masu shigo da kaya na kasashen suna shan wahala.

Ana kuma nuna damuwa a kan yiwuwar wannan al'amari ya zama wani sabon sanadin afkawa matsalar tattalin arziki a duniya.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri