BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 07 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 07:13 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Ba Kudi Ga MDGs Badi A Najeriya
 
Majalisar Tarayyar Najeriya
Hasumiyar Majalisar Dokoki Ta Najeriya
Majalisar Wakilan Najeriya ta yi barazanar cewa ba za ta amince da duk wani kason da bangaren zartarwa zai nemi kebewa shirin muradun karni (MDGs) ba a kasafin kudin shekara mai zuwa.

Wasu 'yan Majalisar dai sun ce bai kamata a kebewa shirin ko da sisin kwabo ba, tunda har yanzu ofishin da ke gudanar da shirin, wanda ke Ofishin Shugaban Kasar, bai kammala aiwatar da wasu ayyukan kasafin kudin shekara ta 2008 ba.

Honorabul Labaran Yunusa Dambatta ya shaidawa wakilin BBC cewa 'yan Majalisar sun yanke wannnan shawara ne don bin kadin hakkin jama'a.

"An sa [ayyukan da ofishin MDGs din ke yi] a cikin kasafin kudin shekarar 2008, wadanda yanzu haka ana yi, da dama ba a gama ba. Saboda haka mu ke ganin lallai ya kamata a ce an gama wadannan. Na bana kuma, wato 2009, har yanzu ba a fara ba", inji Honorabul Dambatta.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri