BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 07 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 07:32 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Alfanun Hakar Uranium A Nijar
 
A Jamhuriyar Nijar, Jihar Agadez, mai nisan kimanin kilomita dubu daya a arewa da babban birnin kasar, Yamai, jiha ce wacce Allah Ya huwace mata arzikin ma'adinai da suka hada da Uranium, wanda ake hako shi a kewayen garin Arlit.

Kuma wannan ma'adani shi ne ke samar da kaso mafi tsoka na kudaden shigar da kasar Nijar din ke samu.

Sai dai bayan kimanin shekaru arba'in na aikin tonon wannan ma'adani da kamfanin Areva na kasar Faransa ya ke gudanarwa, ra'ayoyin wasu 'yan Nijar din sun bambanta a game da alfanun wannan aiki ga jama'a.

Wasu mazauna yankin da wakilin BBC ya zanta da su sun nuna damuwa a kan yadda cututtuka ke karakaina a tsakanin al'umma sakamakon aikin tonon ma'adanan, yayin da wasu kuma ke cewa ayyukan hakar ma'adanan na kawo ci gaba.

Fiye da mutane dubu biyu ne suka samu aikin yi sakamakon hakar ma'adanan.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri