 |
|
| Shugaba Mamadou Tanja na Niger |
Bangarorin siyasa masu hamayya da juna a jamhuriyar Niger na shirye-shiryen zuwa Nigeria, domin tattaunawar neman kawo karshen
rikicin, a karkashin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, ta kasashen yammacin Afirka.
An dai shiga rikicin siyasa ne a kasar ta Niger, tun bayan da Shugaba Tanja ya kuduri aniyar zarcewa da mulki, duk da cewa
kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa yin hakan.
A makon gobe ne ake shirin yin tattaunawar a Abuja, a karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojan Nigeria, Janar Abdussalami
Abubakar mai ritaya, wanda kungiyar ECOWAS ta nada a matsayin mai shiga tsakani.
Dukan bangarorin siyasar Niger din sun ce zasu halarci ganawar.
|