 |
|
| Praministan Birtaniya Gordon Brown |
Praministan Birtaniya, Gordon Brown, ya nemi a bullo da haraji a kan hada-hadar kudade, domin kare duniya daga afkawa cikin
wani rikicin na bankuna.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi ga ministocin kudade na kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki, watau G20,
a St. Andrews, a yankin Scotland.
Mr Brown yace bai yiwuwa ya kasance wasu 'yan kalilan na cin gajiyar ribar da bankuna ke samu, yayin da kuma asara ta fada
kan kowa da kowa.
Masu fafutuka na maraba sosai da wannan shawarar, wadda suka dauka a matsayin wata hanyar tara kudade domin kasashe masu tasowa.
|