BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta:
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Kasashen G20 Zasu Cigaba da Tallafawa Tattalin Arziki
 
Alistair Darling
Sakataren Kudin Birtaniya Alistair Darling
Kasashen duniya masu karfin tattalin arziki da ke cikin kungiyar G20, sun amince su ci gaba da tallafawa tattalin arzikin duniya har ya murmure.

A cikin sanarwar da suka bayar, a karshen taron ministocin kudade na kasashen ashirin, wanda aka yi a Scotland, sun ce ko da yake tattalin arzikin ya dan bunkasa, to amma akwai rashin daidaito a bunkasar.

Musamman ministocin sun nuna damuwa a kan babbar matsalar rashin aikin yi.
Ministan kudin Birtaniya, Alistair Darling, ya ce an sami ci gaba. To amma zasu dauki matakai, ta yadda za a sami ci gaba mai dorewa a shekaru goma masu zuwa.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri