|
Kwararru kan kiwon lafiya sun gano wasu sabbin hanyoyin da za'a bi domin yakar zazzabin cizon sauro a kasashen nahiyar Afirka.
A karshen taron da suka gudanar a birnin Nairobi na kasar Kenya, kwararrun sun ce an samu raguwar cutar a wasu kasashe
da dama a nahiyar, kodayake a kasashe kamar su Nigeria da Ghana, cutar na da da karuwa ne.
Kwararrun sunce akwai bukatar kara tashi tsaye tare da samar da isassun kudade muddin ana son kawadda cutar nan da shekara
ta 2015.
Mutane da dama ne musamman mata da yara ke mutuwa ta sanadiyyar zazzabin cizon sauro a nahiyar Afirka.
|