 |
|
| Sama da sojoji goma sha uku ne aka kashe anan |
An kama wani sojan Amurka bisa wani harbi da aka yi a wani sansanin soji da ke jihar Texas, inda aka halaka mutane goma sha
ukku tare kuma da raunata wasu fiye da talatin.
Wanda aka zarga da yin harbin wani soja ne, kuma likitan lura da hankalin sojojin, mai suna Nidal Malik Hassan.
Hankalin sauran sojojin dake sansanin Fort Hood, inda akai harbin yayi matukar kaduwa, ganin yadda lamarin ya faru.
Wani soja a sansanin ya ce, ba wanda zai taba zatan soja dan uwansa zai taba irin wannan. Abin bakin ciki ne mutum ya
ji ko ya gani."
|