 |
|
| Sansanin Sojoji na Fort Hood |
Shugaba Obama ya yi kira ga jama'ar Amurka da ka da su yi saurin yanke hukuncin game da aniyar wani Manjo na soja da ya bude
wuta a wani barikin soji da ke jihar Texas a jiya Alhamis.
Tuni dai yanzu aka fara gudanar da bincike game da musabbabin wannan harbin da wani hafsan sojin Amurka yayiwa mutane da yawa
a Texas, inda ya kashe sojoji 12 da farar hula daya.
Shugaba Obama ya bukaci Amurkawa da kada su yi riga Malam masallac a kan musabbabin harbin.
Kwamandan sansanin Ford Hood a Texas din ya ce Manjo Nidal Malik Hasan ya bude wuta a kan takarorinsa soji a wani asubiti
kafin shi kansa a harbe shi, inda aka jikkata shi.
|