BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 04 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 15:02 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Dan Sandan Afghanistan ya Kashe Sojojin Birtaniya
 
Birtaniya zata ci gaba da ba jami'an tsaron Afghanistan Horo
Firaministan Birtaniya Gordon Brown
Firaministan Birtaniya, Gordon Brown yace Birtaniya zata cigaba da horar da dakarun tsaro na Afghanistan, duk da kashe sojojinta biyar da wani dan sandan Afghanistan ya yi.

Mr. Brown ya shaidawa majalisar dokokin Birtaniya cewa, kungiyar Taleban tace ita ke da alhakin kai harin, sai dai kuma ba'a san ko sun shiga cikin 'yan sandan ko kuma sun yi amfani da jami'an su ba ne.

Wakilin BBC yace tun kimanin makwannin biyun da suka wuce sojoji ke tare da 'yan sandan Afgahnistan din domin basu horo a lardin Helmand. Sojojin Birtaniya da 'yan sandan Afghanistan din da dama sun jikkata a hari.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri