|
Wata tawaga ta jami'an gwamnatin Nijar ta isa babban birnin Tarayyar Nigeria, Abuja, domin ganawa da mahukuntan kasar, ciki
har da Shugaba Umaru Musa 'Yar Adua.
Masu nazari dai na hasashen cewa, ziyarar ba zata rasa nasaba da irin wadda jami'an Niger din suka kai a kwanan baya ba a
kasashen yammacin Afrika, renon Faransa, tun bayan da kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO, ta dakatar
da kasar daga cikinta.
Tuni Tarayyar Afirka ta goyi bayan matakin da CEDEAO din ta dauka a kan Niger, tare da yin kira a gareta da ta koma mulkin
demokradiyya na zahiri.
|