|
Wata tawagar jami`an gwamnatin janhuriyar Nijar,t a gana da shugaban Najeriya Umaru Musa `Yaradua yau a Abuja.
Tawagar ta hada da Firaministan jamhuriyar Nijar da wasu jami'an gwamnati da dama, wadanda suka je Najeriyar don neman
goyon bayan a sassauta wa Niger din dangane da dakatarwar da kungiyar ECOWAS ko CEDAO tai mata.
A bayan ganawar tasu, tsohon shugaban Nigeria kuma jagoran dake shiga tsakani a rikicin siyasar Niger, janar Abdussalam
Abubakar yace tawagar tazo ne domin neman Nigeria ta shiga tsakanin wajen warware rikicin siyasar Niger din.
A kwanakin baya ma tawagar ta kai irin wannan ziyarar kasashen yammacin Afirka renon Faransa.
|