Skip to main contentAccess keys helpA-Z index
BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 02 Nuwamba, 2009 - An wallafa a 14:59 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
An Bayyana Hamid Karzai a Matsayin Shugaban Afghanistan
 
Zaben Hamid Karzai ya janyo takaddama a Afghanistan
Shugaba Hamid Karzai
Hukumar zaben Afghanistan ta soke zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, kuma ta bayyana shugaba Hamid Karzai a matsayin wanda ya lashe zagayen farko na zaben.

Kakakin hukumar zaben ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai.

Sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya yi maraba da wannan mataki, sannan ya taya Mr Karzai murna.

Wakilin BBC ya ce, yanzu shugaba Hamid Karzai zai cigaba da zama a kan karagar mulki. Hakan dai ya biyo bayan janyewar da abokin hamayyarsa, Abdullah Abdullah ya yi ne, yana mai cewa, za a iya maimaita magudin da aka tafka a zagayen farko.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri