BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 30 Oktoba, 2009 - An wallafa a 17:25 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Hari Kan Peshawar (28 ga Oktoba 2009)
 

Abin da ya biyo bayan hari kan Peshawar, 28 ga Oktoba 2009

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai a birnin Peshawar na Pakistan a ranar Laraba, 28 ga Oktoba 2009. (AFP, AP Photos)

Hari kan Peshawar

Hukumomi sun ce an yi amfani da mota makare da bom ne wajen kai harin. An dai tsaurara tsaro a biranen kasar ta Pakistan.

Hari Kan Peshawar

An kai harin ne a yankin Peepal Mandi na birnin na Peshawar, kuma masu ceto sun yi kokarin kashe gobarar da ta biyo bayan harin.

Hari Kan Peshawar

Jama'a da dama sun kai dauki don ceto rayukan mutane, inda suka yi ta hake tarkace don fito da gawawwaki da kuma wadanda suka samu raunuka.

hari kan Peshawar

Mutane da dama ne dai suka samu raunuka a harin. Kasuwar da aka kai wa harin dai ana sayar da kayayyakin mata ne a cikinta.


 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri