|
Toshe Hanyar Anaca Zuwa Enugu
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
Wasu direbobin manyan motoci sun toshe hanyar Enugu zuwa Anaca ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba bisa zargin tauye hakki.
Babbar hanyar da ta tashi daga Enugu zuwa Anaca, muhimmiyar hanya ce da aka dogara da ita wajen jigilar kayayyaki da zirga-zirga.
Wani direba, mista Ugochukwu Anozie ya shaida wa Abdussalam Ibrahim cewa takurawar da jamian tsaro ke musu ta yi yawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Enugu, Mista Ebere Amaraizu ya musanta zargin da ake wa jami'an 'yan sandan.
Matafiyan da suka saba bin hanyar sun ce, suna ganin fa’idar hakan, wajen raguwar aikata miyagun laifuffuka a hanyar. |
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||