 |
|
| Wani Manomi Na Duba Albarkatun Gonar Sa |
Rahotanni daga jihar Yobe arewacin Najeriya sun nuna cewar an samu bullar annobar farin dango a kananan hukumomi biyar dake
arewacin jihar da suka yi mummunan ta'adi ga amfanin gona masu tarin yawa.
Gwamnatin jihar Yoben ta bayyana cewar sun fara samun rahoton farin ne daga kauyen Maine Kilbuwa dake makwabtaka da Jamhuriyar
Nijar a karamar hukumar Yunusari,kumayanzu haka tana nan tana ci gaba da yakar wadannn fari har ma da wasu kwaruka da kan
dami manoman ta hanyar gudanar da feshi a wadannna yankuna.
Da man dai baya ga karancin ruwan sama Annobar Farin dango da dangoginsu na daga cikin abuwan da sukan haifar da fari a ko
wace shekara musamman a arewacin kasar.
Manoman da dama kan shiga mawuyacin hali kan irin mummuanar asarar amfanin gonar da sukan yi sakamakon irin wadannna matsaloli
da sukan ci karo da su.
|