|
Shawarar Kwararre a kan Salon BBC
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
A cikin wannan fim, wakilin BBC na musamman, Allan Little, ya bayyana yadda yake rubutu a fayyace, da nuna sanin abin da kake magana a kai, don watsawa a rediyo. Ya ce, ana bukatar muhimman abubuwa biyu: ka kasance kana da abin cewa; kana ka fade shi a saukake da harshe marar wuyar ganewa. Kamar kuma yadda Allan ya nuna, idan kana son ka zama marubuci na kwarai, to lalle ka dinga karatu tare da tunani a kan kalaman da aka yi amfani da su a dukkan abin da ka karanta; ka gane wanda ya yi aiki da wanda bai yi ba. Kuma lalle, karara, ka san abin da kake son cimmawa: ba da labari ne, ko bayyana wani yanayi, ko fayyace wani abu mai sarkakkiya. Ko wane yana da salon da ake rubuta shi da shi.
|
WASU SHAFUNAMMU
Rashin Nuna Bambanci03 Maris, 2009 | News
Sanin Ya Kamata03 Maris, 2009 | News
Nahawu03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa03 Maris, 2009 | News
Fassara03 Maris, 2009 | News
Lafazi03 Maris, 2009 | News
Sabbin kalmomi03 Maris, 2009 | News
Suna da Mukami03 Maris, 2009 | News
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||