BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 14:24 GMT
 
Aika ýmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Rashin Nuna Bambanci
 
Rashin Nuna Bambanci

Wanda kake bai wa labari zai yi tsammanin za ka fada masa gaskiya ne iya saninka ba tare da boye-boye ba.

Za ka kawo masa dukkan bangarorin abin da kake ba da labari a kai ba tare da nuna bambanci ga wani ba don ba ka son shi.

A takaice, tamkar ka kulla amana ne tsakaninka da mai sauraro cewa ba za ka yi algushu ba wajen ba shi labari.

Don haka, zai sanya ran jin gaskiyar abin da ka binciko, ko kafarka ta watsa labarai ta biciko, ba wai shaci-fadi ba.

Babu kara gishiri, babu shafa shuni.

Hakan kuwa ba zai yiwu ba sai ka ajiye soyayyarka a gefe guda, kiyayyarka a gefe guda a lokacin da ka zo watsa ma jama’a abin da kake dauke da shi.

Yi hattara da kalmomin muzantawa.

Misali, idan ka ce dubun wani wanda ake zargi ta cika, tamkar ka zartar da hukuncin cewa shi cewa ya dade tabka laifuka ke nan, yanzu kuma Allah ya kama shi.

Ka dai tsaya a kan an kama wani da ake zargi. Amma in kotu ce ta same da laifi, don ka ce yana da laifin ba ka yi laifi ba.

“An cabke...” ta yi kama da abin da kake murnar aukuwarsa, yayin da “an kama...” ba ta da alama nuna ra’ayi.

“An tasa keyarsa...” ta yi kama da wulakanci, yayin da “an kai shi...” ba ta nuna haka ba.

A rahoto ko hira kuma, guji bai wa wani bangare muhimmanci fiye da wani, ko bai wa wani damar fadin ta bakinsa fiye da wani, ko kuma kalubalantar wani fiye da wani a hirarka.

Lalle a ji babu fifita wani a kan wani a duk wani abu da ka watsa.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rubutu don Rediyo
03 Maris, 2009 | News
Sanin Ya Kamata
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Lafazi
03 Maris, 2009 | News
Suna da Mukami
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ýmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri