http://www.bbchausa.com

18 Satumba, 2009 - An wallafa a 13:49 GMT

Shirin Rana

Shirin rana

Rahotanni sun ce, an yi taho-mu-gama da kuma kame-kame a birnin Tehran, yayin da dubban jama'a ke yin maci a wannan ranar da aka kira 'Ranar Kudus'.

Duk da cewa gwamnatin Iran din ce ta shirya macin, shugabannin adawan kasar, wadanda har yanzu ke ja da sake zaben shugaba Mahmoud Ahmadinejad, sun yi kira ga magoya bayansu da su fito.

Hukumomin Iran dai sun ce zasu dauki tsauraran matakai a kan masu tada zaune tsaye.


A Nijeriya, kungiyar 'yan uwa Musulmi, ko 'yan Shi'a a Zaria, jihar Kaduna ta gudanar da Muzahara.

'Yan Shi'ar na yin muzaharar a kowacce shekara, domin nuna bacin ransu, a kan yadda Isra'ila ta mamaye yankunan Falasdinawa, da kuma goyon bayan gwagwarmayar da Falasdinawan ke yi.

A bana hukumomi sun tsaurara matakan tsaro a garin na Zaria, don kaucewa yiwuwar barkewar wani tashin hankali.


Yayin da take gab da kammala ziyarar da ta kai Niger, domin sasanta rikicin siyasar kasar, tawagar majalisar Tarayyar Africa ta gana a yau da 'yan jaridar kasar.

Taron ya maida hankali ne a kan irin rawar da manema labaran ke takawa a zabubukan kasar.

Tun kafin yau dai, tawagar Tarayyar Afirka ta sadu da bangarori daban-daban, ciki har da shugaba Tanja Mamadou, a kokarin da ake na shawo kan kiki-kakan siyasar da ake a Niger din, a kan batun tazarce.